15 Nuwamba 2021 - 17:00
Iran: Babban Kwamandan Hafsan Sojin Ruwan Iran Ya Isa Birnin Paris Halartar Taro Kan Tekun Indiya

Jim kadan kafin barinsa birnin Tehran Rear Admiral shahram Irani ya bayyana wa manema labarai cewa batun tabbatar da tsaro a yankin shi ne babban abin da zai mamaye taron kan tekun indiya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Kasashen dake yankin sun dukufa wajen yin aiki a bangarorin daban daban musamman a bangaren yaki da yan fashin teku, da kuma tabbatar da tsaro da kuma taimakawa jiragen ruwa wajen gudanar da zirga-zirga ba tare da wata matsala ba,

Ana saran zai tattauna da takwarorinsa na kasar game da muhimman batutuwa da suka shafi kasashen, da kuma yadda za’a inganta dangantakar da tsakaninsu day a shafi teku,

Har ila yau ya bayyana cewa harshen teku da ake amfani da shi sanannen abu ne ga dukkan kasashe , kuma yanayin da teku yake ciki ne yake tantance yanayin tsaro da zaman lafiya ga duniya , kuma dukkan kasashen za su iya yin aiki tare ba tare da mai shiga tsakanin ba.

342/